Esta 10:3 - Littafi Mai Tsarki3 Gama sarki Ahasurus kaɗai yake gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama'ar 'yan'uwansa, gama ya nemi lafiyar jama'arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Mordekai mutumin Yahuda, shi ne na biyu a matsayi bayan Sarki Zerzes, mai farin ciki kuma a cikin Yahudawa, aka kuma ɗauke shi da martaba cikin ’yan’uwansa Yahudawa. Gama ya yi aiki don kyautatawar mutanensa, ya kuma yi magana don a kyautata rayuwar dukan Yahudawa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |