idan na sami tagomashi a wurin sarki, idan kuma sarki ya yarda ya biya bukatata da roƙona, to, bari sarki da Haman su zo liyafar da zan yi musu, gobe kuwa zan yi abin da sarki ya faɗa.”
A rana ta bakwai sa'ad da zuciyar sarki take murna saboda ruwan inabi, sai ya umarta bābāninsa guda bakwai, waɗanda suke yi masa hidima, wato Mehuman, da Bizta, da Harbona, da Bigta, da Abagta, da Zetar, da Karkas,