Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 1:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Idan sarki ya yarda, bari ya yi doka, a kuma rubuta ta cikin dokokin Farisa da Mediya don kada a sāke ta, cewa Bashti ba za ta ƙara zuwa wurin sarki Ahasurus ba. Bari sarki ya ba da matsayinta na sarauta ga wata wadda ta fi ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 “Saboda haka, in ya gamshi sarki, bari yă ba da hatimi na sarauta, bari kuma a rubuta shi cikin dokokin Farisa da Mediya, wanda ba za a iya sokewa ba, cewa Bashti ba za tă ƙara zuwa gaban sarkin Zerzes ba. Bari kuma sarki yă ba da matsayinta na sarauta ga wata, wadda ta fi ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 1:19
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ku rubuta doka yadda kuke so da sunan sarki zuwa ga Yahudawa. Ku hatimce ta da hatimin zoben sarki, gama dokar da aka rubuta da sunan sarki, aka kuma hatimce ta da hatimin zoben sarki, ba za a iya a soke ta ba.”


Sai Sama'ila ya ce masa, “Yau Ubangiji ya yage sarautar Isra'ila daga gare ka. Ya ba da ita ga maƙwabcinka wanda ya fi ka.


Esta kuwa ta miƙe tsaye a gaban sarki, ta ce, “Idan sarki ya yarda, idan kuma na sami tagomashi a wurinka, idan ya yi wa sarki kyau, idan kuma sarki yana jin daɗina, bari a yi rubutu a soke wasiƙun da Haman Ba'agage ɗan Hammedata ya rubuta don a hallaka Yahudawan da suke cikin dukan lardunan sarki.


Sai aka kawo dutse aka rufe bakin kogon, sarki kuwa ya hatimce shi da hatiminsa, da hatimin fādawansa, don kada a sāke kome game da Daniyel.


Idan ya gamshi sarki, bari a yi doka a hallaka su, ni kuwa zan ba waɗanda suke tafiyar da aikin sarki, talanti dubu goma (10,000) na azurfa, don su sa a baitulmalin sarki.”


Sa'ad da dukan mutanen Isra'ila suka ji shari'ar da sarki ya yanke, sai suka girmama shi ƙwarai, gama sun gane Allah ya ba shi hikimar daidaita husuma sosai.


Wannan shawara ta gamshi sarki da sauran sarakai, sarki ya yi kamar yadda Memukan ya shawarta.


Yau ma matan Farisa da Mediya waɗanda suka ji abin da sarauniya ta yi, haka za su faɗa wa dukan hakimai. Wannan zai kawo raini da fushi mai yawa.


Bayan waɗannan abubuwa, sa'ad da sarki Ahasurus ya huce daga fushinsa, sai ya tuna da abin da Bashti ta yi, da dokar da aka yi a kanta.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ