Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Esta 1:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Amma sarauniya Bashti ta ƙi zuwa kamar yadda sarki ya umarci bābānin su faɗa mata. Wannan ya sa sarki ya husata ƙwarai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Amma da masu hidima suka ba da umarnin sarki, sai Sarauniya Bashti ta ƙi zuwa. Wannan ya ɓata wa sarki rai, ya kuma yi fushi ƙwarai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Esta 1:12
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hasalar sarki kamar rurin zaki ne, amma alherinsa kamar saukar ruwan sama ne.


Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,


Kamar yadda Ikkilisiya take bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali.


Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa.


Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.


Nebukadnezzar fa, ya husata ya umarta a kawo Shadrak, da Meshak, da Abed-nego. Sai aka kawo su gaban sarki.


Saboda haka sarki ya husata ƙwarai, ya umarta a karkashe duk masu hikima na Babila.


Ka ji tsoron fushin sarki kamar yadda za ka ji tsoron zaki mai ruri, sa shi ya yi fushi kashe kai ne.


Har yaushe za ka yi ta fushi da mu, ya Ubangiji? Har abada ne? Kullum ne fushinka zai yi ta ci kamar wuta?


Don me ka yashe mu haka, ya Allah? Za ka yi ta fushi da jama'arka har abada ne?


Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la'anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya.


Haruna kuwa ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, kada ka ji haushina, ka san jama'an nan sarai da irin halinsu na son aikata mugunta.


Yana kusato zango, sai ya ga siffar ɗan maraƙi, mutane na ta rawa. Musa kuwa ya harzuƙa, ya watsar da allunan da suke hannunsa a gindin dutsen, suka farfashe.


Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”


Sai Nebukadnezzar ya husata ƙwarai da Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, har fuskarsa ta sāke. Sai ya umarta a ƙara zuga wutar, har sau bakwai fiye da yadda take a dā.


su kirawo sarauniya Bashti ta zo wurinsa da kambin sarauta, don ya nuna wa jama'a da shugabanni kyanta, gama ita kyakkyawa ce.


Sarki kuwa ya nemi shawara ga masu hikima waɗanda suka ƙware zamani, gama sarki ya saba da yin haka ga waɗanda suka san doka da shari'a.


Sarki kuwa ya tashi da fushi, ya tafi lambun fāda. Amma Haman ya tsaya don ya roƙi sarauniya Esta ta ceci ransa, gama ya ga sarki yana niyyar hukunta shi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ