Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Daniyel 9:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne mai gafara, amma mu, mun tayar masa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Ubangiji Allahnmu mai jinƙai ne, mai gafartawa ne kuma, ko da yake mun yi masa tawaye;

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Daniyel 9:9
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka.


“Mun yi zunubi, mun yi laifi, mun aikata mugunta, mun yi tawaye. Mun kauce daga bin umarnanka da ka'idodinka.


Ya Ubangiji, kai Allah ne mai jinƙai, mai ƙauna, Mai jinkirin fushi, kullum kai mai alheri ne, mai aminci.


Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji, Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce, A koyaushe yana da nufin yin gafara.


Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.


Amma kakan gafarta mana, Domin mu zama masu tsoronka.


Madawwamiyar ƙauna, ta Ubangiji ce. Kai kanka, ya Ubangiji, kake sāka wa Kowane mutum bisa ga ayyukansa.


Saboda haka ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ina roƙonka, ya Ubangiji, ashe, dā ma can ban faɗa ba, kafin in bar gida, cewa irin abin da za ka yi ke nan? Ai, dalilin da ya sa na yi iyakar ƙoƙarina in gudu zuwa Tarshish ke nan. Na sani kai mai taushin hali ne, mai jinƙai, mai haƙuri. Kai kullum mai alheri ne, a shirye kake kuma ka dakatar da nufinka na yin hukunci.


Zan faɗi ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa, Zan yabe shi saboda dukan abin da ya yi mana. Ya sa wa jama'ar Isra'ila albarka mai yawa, Saboda jinƙansa da ƙaunarsa marar matuƙa.


Bari mugaye su bar irin al'amuransu, Su sāke irin tunaninsu. Bari su juyo wurin Ubangiji, Allahnmu, Shi mai jinƙai ne, mai saurin gafartawa.


Amma mutanen Isra'ila suka tayar mini a cikin jeji, ba su bi dokokina da ka'idodina ba, waɗanda idan mutum ya kiyaye su, zai rayu. Suka ɓata ranar Asabar ƙwarai. Sai na ce zan zubo musu da hasalata, in aukar da fushina a kansu.


Ya Ubangiji, kai managarci ne, mai yin gafara, Cike kake da madawwamiyar ƙauna ga dukan waɗanda suke yin addu'a gare ka.


Duk da haka, saboda yawan jinƙanka, Ba ka yashe su ko ka hallaka su ba. Kai Allah mai alheri ne mai jinƙai!


Sai ka riƙa jin roƙe-roƙen bawanka da na mutanenka Isra'ilawa, idan sun yi addu'a, suna fuskantar wurin nan, sa'ad da ka ji kuma, sai ka gafarta musu.


Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa.


Ya Ubangiji kunya ta rufe mu, mu da sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, saboda mun yi maka zunubi.


Dawuda kuwa ya ce, “Na shiga uku, gara in faɗa a ikon Ubangiji, gama shi mai rahama ne, da in faɗa a ikon mutum.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ