31 Dariyus kuwa Bamediye ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.
31 Dariyus mutumin Medes kuwa ya karɓi mulkin, yana da shekara sittin da biyu.
A shekara ta fari ta sarautar Dariyus ɗan Ahazurus Bamediye wanda ya ci sarautar Kaldiyawa,
Dariyus ya ga ya yi kyau ya naɗa muƙaddas guda ɗari da ashirin a dukan mulkinsa.
Na kafa miki tarko, ya kuwa kama ki, ya Babila, Ke kuwa ba ki sani ba. An same ki, an kama, Domin kin yi gāba da ni.”
Ma'anar PERES ita ce an raba mulkinka, an ba mutanen Mediya da na Farisa.”
“A shekara ta fari ta sarautar Dariyus Bamediye, na tashi na tabbatar da shi, na kuma ƙarfafa shi.”
Zan kawo wa wannan ƙasa dukan abin da na faɗa gāba da ita. Dukan abin da aka rubuta a wannan littafi, wato dukan abin da Irmiya ya yi annabcinsa gāba da dukan al'umman nan.