Daniyel 5:29 - Littafi Mai Tsarki29 Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202029 Sai Belshazar ya umarta, aka sa wa Daniyel riga mai shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”