Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Daniyel 5:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Amma na ji ka iya fassara, ka kuma iya warware al'amura masu wuya. Idan fa ka iya karanta rubutun nan, har kuma ka iya bayyana mini ma'anarsa, to, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin mulkin ƙasar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Na sami labari cewa kana iya ba da fassara da kuma warware matsaloli masu wuya. In har ka iya karanta wannan rubutun ka kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa maka riga shunayya, a kuma sa sarƙar zinariya a wuyanka. Za ka zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Daniyel 5:16
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.”


Sai Belshazzar ya ba da umarni, aka sa wa Daniyel rigar shunayya, aka sa sarƙar zinariya a wuyansa, aka kuma yi shela, cewa yanzu shi ne na uku cikin masu mulkin ƙasar.


Suka ce masa, “Mafarkai muka yi, ba kuma wanda zai fassara mana su.” Sai Yusufu ya ce musu, “Ashe, ba a wurin Allah fassarori suke ba? Ku faɗa mini su, ina roƙonku.”


To, da Saminu ya ga, ashe, ta ɗora hannun manzanni ne ake ba da Ruhun, sai ya miƙa musu kuɗi,


Fir'auna kuwa ya ce wa Yusufu, “Na yi mafarkin da ba wanda ya san fassararsa, amma na ji an ce, wai kai, in ka ji mafarkin kana iya fassara shi.”


Sai Fir'auna ya cire zobensa mai hatimi daga hannunsa ya sa a hannun Yusufu, ya sa masa rigunan lilin masu kyau, ya rataya masa sarƙar zinariya a wuya,


Amma idan kun tuna mini mafarkin, duk da fassararsa, to, zan ba ku lada, da kyautai, da girma mai yawa. Don haka sai ku faɗa mini mafarkin, duk da fassararsa.”


Sai sarki ya ba Daniyel girma mai yawa, da manya manyan kyautai masu yawa. Ya kuma naɗa shi mai mulki bisa dukan lardin Babila. Ya shugabantar da shi bisa dukan masu hikima waɗanda suke Babila.


Sai ya naɗa Daniyel da waɗansu mutum biyu su zama shugabannin muƙaddasan nan. Su muƙaddasan kuwa za su riƙa ba shugabannin labarin aikinsu, don kada sarki ya yi hasarar kome.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ