Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Daniyel 5:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Sarki Belshazzar ya yi wa dubban manyan mutanensa liyafa, ya kuwa sha ruwan inabi a gabansu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Sarki Belshazar ya yi babban biki domin dubban hakimansa ya kuma sha ruwan inabi tare da su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Daniyel 5:1
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta uku ta sarautarsa, sai ya yi biki saboda sarakunansa, da barorinsa, da sarakuna yaƙin Farisa da Mediya, da manyan mutane, da hakiman larduna.


Ubangiji Mai Runduna ya ce mini, “Ko kusa ba za a gafarta musu wannan mugunta ba muddin ransu. Ni, Ubangiji Mai Runduna na faɗa.”


Ubangiji Mai Runduna yana kiranku ku yi kuka, ku yi makoki, ku aske kawunanku, ku sa tsummoki.


Suna maye da abin shansu, Za su ƙone kamar sarƙaƙƙiyar ƙaya, Da busasshiyar ciyawa.


“Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta, Da masu mulkinta, da shugabanninta, Da sojojinta su sha su yi maye. Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna.


Sa'ad da suke cike da haɗama zan yi musu biki, In sa su sha, su yi maye, su yi murna. Za su shiga barcin da ba za su farka ba.


A rana ta uku, wadda take ranar haihuwar Fir'auna, Fir'auna ya yi wa dukan bayinsa biki, sai ya kawo shugaban masu shayarwa da shugaban masu tuya a gaban fādawansa.


Ni Ubangiji na ce, Akwai takobi a kan Kaldiyawa, Da a kan mazaunan Babila, Da a kan ma'aikatanta da masu hikimarta,


A wannan dare kuwa aka kashe Belshazzar Sarkin Kaldiyawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ