28 Wannan duka kuwa ya sami sarki Nebukadnezzar.
28 Duk wannan kuwa ya faru da sarki Nebukadnezzar.
Allah ba kamar mutum ba ne, da zai yi ƙarya, Ba kuwa ɗan mutum ba ne, da zai tuba. Zai cika dukan abin da ya alkawarta, Ya hurta, ya kuwa cika.
Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”
Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”
Abin da mugun yake tsoro, shi yakan auko masa, amma adali yakan sami biyan bukatarsa.
Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.