Daniyel 3:28 - Littafi Mai Tsarki28 Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, wanda ya aiko da mala'ikansa, ya ceci bayinsa masu dogara gare shi, waɗanda kuma ba su yarda su bi umarnin sarki ba, amma suka gwammace a ƙone su maimakon su bauta wa gunki, ko su yi masa sujada, sai dai ga Allahnsu kaɗai. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202028 Sa’an nan Nebukadnezzar ya ce, “Yabo ya tabbata ga Allahn Shadrak, Meshak da Abednego wanda ya aiko da mala’ikansa ya ceci bayinsa da suka dogara matuƙa a gare shi, suka ki bin umarnin sarki kuma su na a shirye domin su ba da ransu da suka ƙi bauta ko su yi sujada ga wani allah sai dai Allahnsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.