Daniyel 2:37 - Littafi Mai Tsarki37 Ya sarki, kai ne sarkin sarakuna wanda Allah na Sama ya ba ka sarauta, da iko, da ƙarfi, da daraja. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202037 Ya, sarki, kai ne sarkin sarakuna. Allah na sama ya ba ka iko da girma da suna; အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.