Daniyel 2:28 - Littafi Mai Tsarki28 Amma akwai Allah a Sama mai bayyana asirai, shi ne ya sanar wa sarki Nebukadnezzar da abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayinka waɗanda suka zo cikin tunaninka, sa'ad da kake kwance bisa gadonka ke nan. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202028 amma akwai Allahn da yake a sama wanda yake bayyana asirai, ya nuna wa sarki Nebukadnezzar abin da zai faru a kwanaki masu zuwa. Mafarkinka da wahayin da ya wuce cikin tunaninka a sa’ad da kake kwance a gadonka su ne, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bayan kwanaki masu yawa zan ziyarce ka, a cikar waɗannan shekaru, za ka koma ƙasar duwatsun Isra'ila, wadda ta farfaɗo daga masifar yaƙin da ta sha, ƙasa inda jama'a suka tattaru daga sauran al'umma masu yawa, wadda a dā ta yi ta lalacewa, sai da aka fito da mutanenta daga cikin al'ummai, yanzu kuwa dukansu suna zaman lafiya.