42 Zai kai wa waɗansu ƙasashe yaƙi, ƙasar Masar kuwa ba za ta kuɓuta ba.
42 Zai fadada mulkinsa har zuwa ƙasashe masu yawa; Masar ma ba za tă tsira ba.
a kuma bar gawawwakinsu a kan hanyar babban birnin nan da ake kira Saduma da Masar ga ma'ana ta ruhu, a inda aka gicciye Ubangijinsu.
Idan kuwa wata al'umma a duniya ba ta haura zuwa Urushalima domin ta yi wa Ubangiji Maɗaukakin Sarki sujada ba, ba za a yi mata ruwan sama ba.
Zan komo da Masarawa, in maido su a ƙasar Fatros, ƙasarsu ta ainihi. Za su zama mulki marar ƙarfi.
Zai shiga kyakkyawar ƙasa ya kashe dubban mutane. Amma ƙasar Edom, da ta Mowab, da yawancin ƙasar Ammonawa za su kuɓuta daga hannunsa.
Zai mallaki dukiyoyi na zinariya, da na azurfa, da dukan abubuwa masu tamani na Masar. Zai kuma ci Libiyawa da Habasha da yaƙi.