Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Daniyel 11:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Zai yunƙuro da dukan ƙarfin mulkinsa, zai zo ya gabatar da shawarar salama, ya aikata ta. Zai aurar masa da 'yarsa don ta lalatar da mulkin abokin gabansa, amma wannan dabara ba za ta ci ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Zai yunƙura yă zo da ƙarfin dukan masarautarsa zai kuma nemi haɗinkan sarkin Kudu. Zai kuma ba shi diyarsa yă aura don yă lalatar da mulkin, amma shirinsa ba zai yi nasara ba ko yă taimake shi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Daniyel 11:17
15 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Za ka fuskanci Urushalima wadda aka kewaye ta da yaƙi da hannunka a zāge, sa'an nan ka yi annabci a kanta.


Ka ɗauki kwano, ka shirya shi kamar garun ƙarfe tsakaninka da birnin, sa'an nan ka zuba ido. Birnin zai zama kamar an kewaye shi da yaƙi, kai kuwa ka kewaye shi da yaƙi. Wannan kuma zai zama alama ga Isra'ilawa.


Hazayel Sarkin Suriya kuwa ya tafi ya yi yaƙi da Gat har ya cinye ta, ya kuma shirya zai yi yaƙi da Urushalima.


To, me kuma za mu ce a game da haka? Da yake Allah yana goyon bayanmu, wa kuwa zai iya gāba da mu?


Wanda ba nawa ba ne, gāba yake yi da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.”


Da lokacin karɓarsa a Sama ya gabato, ya himmantu sosai ga zuwa Urushalima.


Wanda ba nawa ba ne, gāba yake da ni. Wanda kuma ba ya taya ni tarawa, watsarwa yake yi.


Sa'an nan zai juya, ya nufi kagarar ƙasarsa, amma zai yi tuntuɓe, ya fāɗi, ba za a ƙara ganinsa ba.”


Za ta kasance har shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu, sa'an nan za a kashe Masihan, ba zai sami kome ba. Jama'ar shugaban da zai zo za su hallaka birnin da Haikali. A ƙarshensa za a yi rigyawa, da yaƙe-yaƙe, da hallakarwa kamar yadda aka ƙaddara.


“Ɗan mutum, ka fuskanci wajen Ammonawa, ka yi annabci a kansu.


Fir'auna da yawan sojojinsa masu ƙarfi, ba za su taimake shi da yaƙin ba, sa'ad da Babilawa suka gina mahaurai da kagarai don su kashe mutane da yawa.


Mutum ya iya shirya dabaru iri iri, amma sai nufin Ubangiji ne zai tabbata.


A ranar da na yi kira gare ka, Za a komar da abokan gābana baya, Gama na sani Allah yana tare da ni!


Sai Yehoshafat ya ji tsoro ya himmatu ga neman Ubangiji, ya kuma sa a yi shela, a yi azumi a dukan Yahuza.


“Sun zo don su yi kama-karya. Ana jin tsoronsu tun ma kafin su zo. Sun tattara bayi kamar yashi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ