Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Daniyel 10:9 - Littafi Mai Tsarki

9 Sa'an nan na ji muryarsa, da jin muryarsa, sai na faɗi rubda ciki, barci mai nauyi ya kwashe ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Sai na ji yana magana, da ina sauraronsa, sai na shiga barci mai nauyi, na kuwa fāɗi rubda ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Daniyel 10:9
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da yake magana da ni, sai barci mai nauyi ya kwashe ni da nake kwance rubda ciki, amma sai ya taɓa ni, ya tashe ni tsaye.


Kamar wani irin mafarki mai razanarwa yake, Wanda ya hana ni jin daɗin barcina.


Sa'ad da rana take faɗuwa, barci mai nauyi ya kwashe Abram, sai ga babban duhu mai bantsoro ya rufe shi.


Da ya tashi daga addu'a, ya koma wurin almajiran, ya tarar suna barci saboda baƙin ciki.


Sai kuma Bitrus da waɗanda suke tare da shi, barci ya cika musu ido, amma da suka farka suka ga ɗaukakarsa, da kuma mutum biyun nan tsaye tare da shi.


Ina barci, amma zuciyata na a farke, Sai na ji ƙaunataccena yana ƙwanƙwasa ƙofa. Buɗe mini in shigo, ƙaunatacciyata, budurwata, kurciyata, Wadda ba wanda zai kushe ki. Kaina ya jiƙe da raɓa, Gashina ya yi danshi da laimar ƙāsashi.


Yakan sanar a mafarkai ko a wahayi Sa'ad da barci mai nauyi ya ɗauke su, A sa'ad da suke barci a gadajensu.


Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama,


Da na gan shi, sai na fāɗi a gabansa kamar na mutu. Amma ya ɗora mini hannunsa na dama, ya ce, “Kada ka ji tsoro. Ni ne na Farko. Ni ne na Ƙarshe,


Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi.


Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa, Leɓunana suka raurawa. Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki. Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ