Daniyel 10:16 - Littafi Mai Tsarki16 Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Sai wani wanda ya yi kama da mutum ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Daniyel kuwa wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar, ya tsaya zugum da ɗan daɗewa, tunaninsa ya ba shi tsoro. Sarki ya ce, “Belteshazzar, kada ka bar mafarkin ko ma'anarsa ya ba ka tsoro.” Sai Belteshazzar ya amsa, ya ce, “Ya shugabana, Allah ya sa mafarkin nan, da ma'anarsa, su zama a kan maƙiyanka.