Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Daniyel 1:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Da sarki ya yi magana da su, sai ya tarar a cikinsu duka, ba wani kamar Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya. Don haka aka maishe su 'yan majalisar sarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 Sarki kuwa ya yi magana da su, sai ya gano cewa babu wani kamar Daniyel, Hananiya, Mishayel da kuma Azariya; don haka sai suka shiga yi wa sarki hidima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Daniyel 1:19
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sarki kuwa ya sa a riƙa ba su abinci da ruwan inabi irin nasa kowace rana. A kuma koyar da su har shekara uku. Bayan shekara uku za su shiga yi wa sarki hidima.


Ka nuna mini mutumin da yake aiki mai kyau, ni kuwa in nuna maka mutumin da ya fi duka, wanda ya cancanci ya zauna tare da sarakuna.


Yusufu yana da shekara talatin lokacin da ya kama aiki a wurin Fir'auna, Sarkin Masar. Yusufu kuwa ya fita daga gaban Fir'auna ya ratsa dukan ƙasar Masar.


“Domin haka ga abin da ni, Ubangiji na ce, Idan ka komo sa'an nan zan kawo ka. Za ka tsaya a gabana. Idan ka hurta abin da yake gaskiya ba na ƙarya ba, Za ka zama kakakina. Za su komo gare ka, Amma kai ba za ka koma wurinsu ba.


Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”


A cikin waɗanda aka zaɓa akwai Daniyel, da Hananiya, da Mishayel, da Azariya, daga kabilar Yahuza.


Sai sarkin fāda ya laƙaba musu sababbin sunaye. Ya kira Daniyel, Belteshazzar, ya kira Hananiya, Shadrak, ya kira Mishayel, Meshak, sa'an nan ya kira Azariya, Abed-nego.


Sa'ad da lokacin da sarki ya ƙayyade ya ƙare, sarkin fāda ya gabatar da su a gaban Nebukadnezzar.


Sai doka ta fita cewa a karkashe masu hikima. Aka nemi Daniyel da abokansa don a kashe su.


Domin haka ina ba da wannan umarni cewa, ‘Dukan jama'a, ko al'umma, ko harshe wanda zai yi saɓon Allah na Shadrak, da Meshak, da Abed-nego, za a yanyanka su gunduwa gunduwa, a ragargaje gidajensu, gama ba wani allah wanda zai yi wannan irin ceto.’ ”


su kasance samari ne kyawawa, waɗanda ba su da wata naƙasa, masu fasaha cikin kowane abu, masu fahimta, da masu saurin ganewa, waɗanda suke da halin iya hidima a fādar sarki. Nebukadnezzar ya umarci Ashfenaz ya koya musu littattafan Kaldiyawa da harshen Kaldiyawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ