Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 9:40 - Littafi Mai Tsarki

40 Amma Bitrus ya fitar da su duka waje, ya durƙusa, ya yi addu'a. Ya juya wajen gawar, ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe ido, da ta ga Bitrus, ta tashi zaune.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

40 Bitrus ya fitar da su duka daga ɗakin; sa’an nan ya durƙusa ya yi addu’a. Da ya juya wajen matacciyar, sai ya ce, “Tabita, tashi.” Ta buɗe idanunta, ta ga Bitrus sai ta tashi zaune.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 9:40
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma da aka fitar da taron waje, ya shiga ya kama hannunta, sai kuwa yarinyar ta tashi.


Sa'an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.


Shi kuwa sai ya riƙe hannunta, ya ta da murya ya ce, “Yarinya, ki tashi.”


Da Bulus ya faɗi haka, ya durƙusa, duka suka yi addu'a tare.


Sai ya ɗan rabu da su misalin nisan jifa, ya durƙusa, ya yi addu'a.


Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.”


Amma da lokacin tashinmu ya yi, muka tashi muka ci gaba da tafiyarmu, dukansu kuma har da matansu da 'ya'yansu, suka raka mu bayan gari, sa'an nan muka durƙusa a kan gaci, muka yi addu'a, muka yi bankwana da juna.


Amma in za ka yi addu'a, sai ka shiga lollokinka, ka rufe ƙofa, ka yi addu'a ga Ubanku wanda yake ɓoye, Ubanku kuwa da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.


Ashe, uban Babiliyas yana a kwance, yana fama da zazzaɓi da atuni. Sai Bulus ya shiga wurinsa ya yi addu'a, ya ɗora masa hannu ya warkar da shi.


Sai annabi Ishaya ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya komar da inuwa baya da taki goma, bayan da ta riga ta wuce a matakin sarki Ahaz.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ