Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.
Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin 'yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al'ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin 'yan'uwa na ƙarya.
ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa'ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.