An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.
Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Tayatira haka, ‘Ga maganar Ɗan Allah, mai idanu kamar harshen wuta, mai ƙafafu kamar gogaggiyar tagulla.
Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”
Sai Bulus da Barnaba suka yi magana gabagaɗi, suka ce, “Ku, ya wajaba a fara yi wa Maganar Allah, amma da yake kun ture ta, kun nuna ba ku cancanci samun rai madawwami ba, to, za mu juya ga al'ummai.