Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 9:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Sai ya ci abinci, ƙarfinsa kuma ya komo. Shawulu kuwa ya yi 'yan kwanaki tare da masu bi da suke Dimashƙu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 bayan ya ci abinci, sai sāke samun ƙarfi. Shawulu ya yi kwanaki masu yawa tare da almajiran da suke a Damaskus.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 9:19
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da fari, na yi wa mutanen Dimashƙu wa'azi, sa'an nan na yi a Urushalima da dukan kewayen ƙasar Yahudiya, sa'an nan kuma na yi wa al'ummai, cewa su tuba su juyo ga Allah, su kuma yi aikin da zai nuna tubarsu.


Suka kuma ba shi kauɗar ɓaure da nonnan inabi biyu. Da ya ci sai ya wartsake, gama ya yi yini uku da dare uku ba ci ba sha.


ban kuma je Urushalima wurin waɗanda suka riga ni zama manzanni ba, sai nan da nan na je ƙasar Larabawa, sa'an nan na komo Dimashƙu.


bayan ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antakiya. Shekara sur suna taruwa da Ikkilisiya, suna koya wa mutane masu yawan gaske. A Antakiya ne aka fara kiran masu bi da suna Kirista.


Yi tafiyarka, ka ci abincinka da farin ciki, ka sha ruwan inabinka da fara'a, gama abin da ka yi duka daidai ne a wurin Allah.


Nan take sai wani abu kamar ɓawo ya faɗo daga idanunsa, sai ya sāke gani. Sa'an nan ya tashi, aka yi masa baftisma.


Da ya zo Urushalima ya yi ƙoƙarin shiga cikin masu bi, amma duk suka ji tsoronsa, don ba su gaskata shi mai bi ba ne.


Da yake Lidda kusa da yafa take, da masu bi suka ji Bitrus na can, suka aiki mutum biyu wurinsa, su roƙe shi ya zo wurinsu ba da jinkiri ba.


Sai masu bi suka ɗaura niyya, kowa gwargwadon ƙarfinsa, su aika wa yan'uwan da suke ƙasar Yahudiya gudunmawa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ