Da ya zo gare mu, ya ɗauki ɗamarar Bulus ya ɗaure kansa sawu da hannu, ya ce, “Ga abin da Ruhu Mai Tsarki ya ce, ‘Haka Yahudawan Urushalima za su ɗaure mai wannan ɗamara, su kuma bashe shi ga al'ummai.’ ”
Ku tuna da maganar da na yi muku cewa, “Bawa ba ya fin ubangijinsa.” In sun tsananta mini, ku ma za su tsananta muku. Da sun kiyaye maganata, da sai su kiyaye taku ma.
Saboda haka, ne nake shan wuya haka. Duk da haka, ban kunyata ba, domin na san wanda na gaskata da shi, na kuma tabbata yana da iko ya kiyaye abin da na danƙa masa, har ya zuwa waccan rana.
da kuma yawan tsanani, da wuyar da na sha, da suka same ni a Antakiya, da Ikoniya, da Listira, wato irin tsanance-tsanancen da na jure. Amma Ubangiji ya kuɓutar da ni daga cikinsu duka.
Ni ne Yahaya, ɗan'uwanku abokin tarayyarku a cikin tsanani, da mulki, da jimiri da suke a cikin Yesu. Ina a can tsibirin da ake kira Batamusa saboda Maganar Allah da kuma shaidar Yesu.
Magabtanmu sun shiga uku! Sun yi fashi sun ci amana, ko da yake ba wanda ya yi musu fashi ko cin amana. Amma lokacinsu na fashi da na cin amana zai ƙare, su ne kuma za a yi wa fashi da cin amana.
Sai Bulus ya amsa ya ce, “Me ke nan kuke yi, kuna kuka kuna baƙanta mini rai? Ai, ni a shirye nake, ba wai a ɗaure ni kawai ba, har ma a kashe ni a Urushalima saboda sunan Ubangiji Yesu.”