8 Saboda haka aka yi ta farin ciki a garin ƙwarai da gaske.
8 Saboda haka aka yi farin ciki ƙwarai a birnin.
Amma kuwa masu bi suna farin ciki matuƙa, suna kuma a cike da Ruhu Mai Tsarki.
Da al'ummai suka ji haka, suka yi farin ciki, suka ɗaukaka Maganar Ubangiji, ɗaukacin kuma waɗanda aka ƙaddara wa samun rai madawwami suka ba da gaskiya.
Da suka fito daga ruwan, Ruhun Ubangiji ya fauce Filibus, bābān kuma bai ƙara ganinsa ba. Sai ya yi ta tafiya tasa yana farin ciki.
Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan.