To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin nan da ya tashi kan sha'anin Istifanas, sun yi tafiya har ƙasar Finikiya, da tsibirin Kubrus, da birnin Antakiya, ba su yin wa'azin Maganar Allah ga kowa sai ga Yahudawa kaɗai.
Shawulu kuwa yana goyon bayan kisan Istifanas. A ran nan kuwa wani babban tsanani ya auko wa Ikkilisiyar da take Urushalima. Duk aka warwatsa su a lardin Yahudiya da na Samariya, sai dai manzannin kawai.
Amma ko da yake dā ma can mun sha wuya, an kuma wulakanta mu a Filibi, kamar yadda kuka sani, duk da haka da taimakon Allahnmu muka sanar da ku bisharar Allah gabagaɗi, amma sai da matsanancin fama.