“To, ba irin wannan azumi ne na zaɓa ba? Wato ku kwance sarƙoƙin mugunta, ku kwance masu karkiya, ku 'yantar da waɗanda ake zalunta, ku kakkarye kowace karkiya.
Da yake Allah bai rangwanta wa mala'iku ba sa'ad da suka yi zunubi, sai ya jefa su a Gidan Wuta, ya tura su a cikin ramummuka masu zurfi, masu baƙin duhu, a tsare su har ya zuwa ranar hukunci,
Mu kanmu ma dā can mun yi wauta, mun kangare, an ɓad da mu, mun jarabta da muguwar sha'awa da nishaɗi iri iri, mun yi zaman ƙeta da hassada, mun zama abin ƙi, mu kuma mun ƙi waɗansu.
Kada ku yi dariya saboda faɗakarwar da nake yi muku! Idan kuwa kun yi, zai ƙara yi muku wuya ku tsira. Na ji niyyar da Ubangiji Mai Runduna ya yi, ta ya hallaka dukan ƙasar.