“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.
Ashe, ba ka sani ba? Ashe, ba ka ji ba? Ubangiji Madawwamin Allah ne? Ya halicci dukkan duniya. Bai taɓa jin gajiya ko kasala ba. Ba wanda ya taɓa fahimtar tunaninsa.
Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.
“Ni ne Ubangiji, Mahaliccinku, Mai Fansarku. Ni ne Ubangiji, Mahaliccin dukkan abu. Ni kaɗai na shimfiɗa sammai, Ba wanda ya taimake ni sa'ad da na yi duniya.