Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 7:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Amma kuwa shi kansa, bai ba shi gādonta ba, ko da taki ɗaya, sai dai ya yi masa alkawari zai mallakar masa ita, shi da zuriyar bayansa, ko da yake ba shi da ɗa a lokacin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Bai ba shi gādo a nan ba, ko taki ɗaya na ƙasa. Amma Allah ya yi masa alkawari cewa shi da zuriyarsa masu zuwa bayansa za su mallaki ƙasar, ko da yake a lokacin Ibrahim ba shi da yaro.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 7:5
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Zan ba ka, kai da zuriyarka a bayanka, ƙasar baƙuncinka, wato dukan ƙasar Kan'ana ta zama mallakarka har abada, ni kuwa zan zama Allahnsu.”


Sai Ubangiji ya bayyana ga Abram, ya ce, “Ga zuriyarka zan ba da wannan ƙasa.” Sai ya gina bagade ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.


A wannan rana Ubangiji ya yi wa Abram alkawari ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga Kogin Masar zuwa babban kogi, wato Kogin Yufiretis ke nan,


gama dukan ƙasan nan da kake gani kai zan ba, da zuriyarka har abada.


Ka yi baƙunci cikin wannan ƙasa, ni kuwa zan kasance tare da kai, zan sa maka albarka, gama a gare ka da zuriyarka ne na ba da waɗannan ƙasashe, zan kuwa cika rantsuwar da na yi wa Ibrahim mahaifinka.


Ka iske shi amintacce a gare ka, Ka kuwa yi masa alkawari. Ka yi alkawari za ka ba shi ƙasar Kan'ana, Da ta Hittiyawa, da ta Amoriyawa, da ta Ferizziyawa, Da ta Yebusiyawa, da ta Girgashiyawa, Ta zama inda zuriyarsa za su zauna. Ka kuwa cika alkawarinka, gama kai mai aminci ne.


Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”


domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji ya rantse zai ba kakanninku da zuriyarsu, ƙasar da yake da yalwar abinci.


Sai Ubangiji ya ce mini, ‘Tashi, ka tafi, ka kama tafiyarka a gaban jama'an nan domin su je, su shiga, su mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.’ ”


Ba saboda adalcinku, ko kuma gaskiyarku ne ya sa za ku shiga ƙasar, ku mallake ta ba, amma saboda muguntar waɗannan al'ummai ne, Ubangiji Allahnku ya kore su a gabanku domin kuma ya cika maganar da ya rantse wa kakanninku, wato su Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.


kada ku tsokane su, gama ko wurin sa ƙafa a ƙasarsu ba zan ba ku ba, gama na riga na ba Isuwa ƙasar tuddai ta Seyir.


“Ni baƙo ne, ina tsakaninku, ina zaman baƙunci. Ku sayar mini da wurin yin makabarta, domin in binne matata, in daina ganinta!”


Sai Saraya ta ce wa Abram, “To, ga shi, Ubangiji ya hana mini haihuwar 'ya'ya. Shiga wurin baranyata, mai yiwuwa ne in sami 'ya'ya daga gare ta.” Abram kuwa ya saurari murya matarsa Saraya.


“Ɗan mutum, mazaunan wuraren nan da aka lalatar a ƙasar Isra'ila, suna cewa, ‘Ibrahim shi kaɗai ne, duk da haka an ba shi ƙasar duka, balle fa mu da muke da yawa, lalle ƙasar tamu ce.’


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ