Yanzu Ubangiji ya cika alkawarin da ya yi, gama na tashi a maimakon tsohona, Dawuda, na hau gadon sarautar Isra'ila, kamar yadda ya alkawarta, ga shi kuwa, na gina Haikali saboda Ubangiji Allah na Isra'ila.
Sulemanu kuwa ya fara ginin Haikalin Ubangiji a Urushalima a kan Dutsen Moriya, inda Ubangiji ya taɓa bayyana ga tsohonsa Dawuda, inda kuma Dawuda ya riga ya shirya a daidai masussukar Arauna Bayebuse.
Sa'ad da Dawuda yake zaune a fādarsa, sai ya ce, wa annabi Natan, “Ga shi, ni ina zaune a cikin gidan da aka yi da itacen al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana cikin alfarwa.”
A shekara ta arbaminya da tamanin bayan fitowar mutanen Isra'ila daga ƙasar Masar, a shekara ta huɗu ta sarautar Sulemanu, Sarkin Isra'ila, a watan biyu, wato watan Zib, sai Sulemanu ya fara gina Haikalin Ubangiji.