Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 7:38 - Littafi Mai Tsarki

38 Shi ne kuma wanda yake a cikin Ikkilisiyar nan a jeji tare da mala'ikan da ya yi masa magana a Dutsen Sinai, tare da kakanninmu kuma. Shi ne kuma ya karɓo rayayyiyar magana domin ya kawo mana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

38 Ya kasance a cikin taron nan a hamada, tare da mala’ikan da ya yi magana da shi a Dutsen Sinai, da kuma tare da kakanninmu; ya kuma karɓi kalmomi masu rai don yă miƙa mana.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 7:38
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ai kuwa, akwai ƙwarai, ta kowace hanya. Da farko dai, Yahudawa su ne aka amince wa a game da zantuttukan Allah.


Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba.


Duk mai wa'azi yă dai san faɗar Allah yake yi. Duk mai yin hidima, yă yi da ƙarfin da Allah ya ba shi, domin a cikin al'amura duka a ɗaukaka Allah ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka da mulki sun tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!


ku ne kuwa kuka karɓi Shari'a ta wurin mala'iku, amma ba ku kiyaye ta ba!”


Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.


Musa ya ba mu dokoki, Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu.


daga dukan wahalar da suke sha. Ba mala'ika ne ya cece su ba, amma Ubangiji ne. Da ƙaunarsa da juyayinsa ya fanshe su. A koyaushe yake lura da su a dā,


Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta.


In kuwa maganar nan da aka faɗa ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowane keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su,


To, mece ce manufar Shari'a? Ƙari aka yi da ita don fitowa da laifi fili, har kafin na zuriyar nan ya zo, wanda aka yi wa alkawarin, an kuma ba da ita ta wurin mala'iku ne, ta hannun matsakanci.


Su ne Isra'ilawa. Da zama 'ya'yan Allah, da ganin ɗaukakarsa, da alkawaran nan, da baiwar Shari'a, da ibada, da kuma sauran alkawarai, duk nasu ne.


“To, shi Musan nan da suka ƙi, suna cewa, ‘Wa ya sa ka shugaba kuma alƙali?’ shi ne Allah ya aiko ya zama shugaba, da mai ceto, ta taimakon mala'ikan nan da ya bayyana a gare shi a cikin kurmin nan.


“To, bayan shekara arba'in, wani mala'ika ya bayyana a gare shi cikin harshen wuta, a wani kurmi a jejin Dutsen Sina'i.


Ai, Ruhu shi ne mai rayarwa, jiki kam ba ya amfana kome. Kalmomin da na faɗa muku ruhu ne, da kuma rai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ