Ayyukan Manzanni 6:1 - Littafi Mai Tsarki1 To, a kwanakin nan da yawan masu bi suke Ƙaruwa, sai Yahudawa masu jin Helenanci suka yi wa Ibraniyawa gunaguni domin bā a kula da matayensu waɗanda mazansu suka mutu, a wajen rabon gudunmawa a kowace rana. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20201 A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan zo wurinku domin in yi shari'a. Nan da nan zan tabbatar da laifin masu yin sihiri, da na mazinata, da na masu shaidar zur, da na masu zaluntar ma'aikata a kan albashinsu, da waɗanda suke ƙwarar gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu, da marayu, da baƙi, da waɗanda ba su ganin girmana.”