Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 5:34 - Littafi Mai Tsarki

34 Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama'a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

34 Amma wani Bafarisiyen da ake kira Gamaliyel, wani malamin doka, wanda dukan mutane ke girmamawa, ya miƙe tsaye a Majalisar ya umarta a fitar da mutanen waje na ɗan lokaci.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 5:34
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

“Ni bayahude ne, haifaffen Tarsus, ƙasar Kilikiya, amma a nan garin na girma, aka kuma karantar da ni wurin Gamaliyal, bisa ga tsarin tsanantacciyar hanyar nan ta Shari'ar kakanninmu. Ina mai himmar bauta wa Allah, kamar yadda dukanku kuke a yau,


Sai kuma a rana uku suka same shi a Haikalin zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu, yana kuma yi musu tambayoyi.


Wata rana na koyarwa, waɗansu Farisiyawa kuwa da masanan Attaura da suka fito daga kowane gari na ƙasar Galili, da na ƙasar Yahudiya, daga kuma Urushalima, suna nan a zaune. Ikon Ubangiji na warkarwa kuwa yana nan.


Hasalar mutane ba ta ƙara kome, sai dai ta ƙara maka yabo. Waɗanda suka tsira daga yaƙe-yaƙe za su kiyaye idodinka.


Bayan sun umarce su, su fita daga majalisa, suka yi shawara da juna,


Sarakuna kuwa da dukan jama'a suka ce wa firistoci da annabawa, “Wannan mutum bai yi abin da ya isa hukuncin kisa ba, gama ya yi magana da sunan Ubangiji Allahnmu.”


Sai waɗansu daga cikin dattawan ƙasar suka miƙe tsaye, suka ce wa dukan taron jama'a,


Ko da yake Elnatan, da Delaiya, da Gemariya, sun faɗa wa sarki kada ya ƙone littafin, amma ya yi biris da su.


Yesu ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai ma da kake malamin Isra'ila, ba ka fahimci waɗannan al'amura ba?


Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa. To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra'ilawa, suka aika kurkuku a kawo su.


Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su,


Sa'an nan ya ce musu, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, ku kula fa da abin da kuke niyyar yi wa mutanen nan.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ