Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 5:24 - Littafi Mai Tsarki

24 To, da shugaban dogaran Haikali da manyan firistocin suka ji haka, suka ruɗe ƙwarai a game da su, suka rasa inda abin zai kai.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Da jin wannan labari, sai shugaban masu gadin haikali da manyan firistocin suka ruɗe, suna tunanin abin da wannan al’amari zai zama.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 5:24
17 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai shugaban dogaran Haikali da dogaran suka je suka kawo manzannin, amma fa ba ƙarfi da yaji ba, don suna tsoro kada jama'a su jejjefe su da duwatsu.


Suna cikin yin magana da jama'a sai firistoci da shugaban dogaran Haikali da Sadukiyawa suka ji haushi ƙwarai, suka aukar musu,


Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama'a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.


Duk kuwa suka yi mamaki, suka ruɗe, suna ce wa juna, “Me ke nan kuma?”


Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”


Yesu kuma ya ce wa waɗanda suka tasar masa, wato, manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali da shugabannin jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake, kamar masu kama ɗan fashi?


Sai ya tafi ya yi shawara da manyan firistoci da shugabannin dogaran Haikali a kan yadda zai bāshe shi a gare su.


Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.


“Mun iske kurkukun a kulle sosai, masu tsaro kuma na tsaro a bakin ƙofofin, amma da muka buɗe, sai muka tarar ba kowa a ciki.”


Sai wani ya zo ya ce musu, “Ai, ga shi, mutanen nan da kuka sa a kurkuku suna nan a tsaye a Haikali, suna koya wa jama'a.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ