Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 5:21 - Littafi Mai Tsarki

21 Da suka ji haka, suka shiga Haikalin da sassafe, suna koyarwa. To, babban firist ya fito, shi da waɗanda suke tare da shi, suka kira majalisa, da dukan shugabannin Isra'ilawa, suka aika kurkuku a kawo su.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

21 Da gari ya waye, sai suka shiga filin haikali, yadda aka faɗa musu, suka kuwa fara koyar da mutane. Sa’ad da babban firist da abokan aikinsa suka iso, sai suka kira Majalisa gaba ɗaya dukan dattawan Isra’ila, suka kuma aika kurkuku a zo da manzannin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 5:21
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da sassafe kuma ya sāke shiga Haikali. Duk mutane suka zo wurinsa, ya kuwa zauna yana koya musu.


Don za ka zama mashaidinsa ga dukan mutane game da abin da ka gani, ka kuma ji.


To, suka tashi daga gaban majalisar, suna farin ciki a kan an ga sun isa su sha wulakanci saboda sunan Yesu.


Amma wani Bafarisiye, wai shi Gamaliyal, masanin Attaura, wanda duk jama'a suke girmamawa, ya miƙe cikin majalisa, ya yi umarni a fitar da mutanen nan waje tukuna.


Da suka kawo su, suka tsai da su a gaban majalisar. Sai babban firist ya tambaye su,


Amma babban firist ya taso, da duk waɗanda suke tare da shi, wato 'yan ɗariƙa Sadukiyawa, suna kishi gaya,


Bilatus ya amsa ya ce, “Ni Bayahude ne? Ai, jama'arku da manyan firistoci su ne suka bāshe ka gare ni. Me ka yi?”


Da gari ya waye sai majalisar shugabannin jama'a ta haɗu, da manyan firistoci da kuma malaman Attaura. Suka kai shi ɗakin majalisarsu suka ce,


Amma ni ina gaya muku, kowa yake fushi da ɗan'uwansa ma, za a hukunta shi. Kowa ya ce da ɗan'uwansa wawa, za a kai shi gaban majalisa. Kowa kuma ya ce, ‘Kai wofi!’ hakkinsa shiga Gidan Wuta.


Ya ba shi cikakken iko bisa dukan ma'aikatan hukuma. Ya ba shi ikon umartar mashawartansa.


Babban firist ma da dukan majalisar shugabannin jama'a za su iya shaidata, daga gunsu ne kuma na karɓi wasiƙu zuwa ga 'yan'uwanmu Yahudawa, na tafi Dimashƙu, don in ɗebo waɗanda suke can ma, in zo da su Urushalima a ɗaure, a azabta su.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ