In su bayin Almasihu ne, ni na fi su ma, ina magana kamar ruɗaɗɗe ne fa! ai, na fi su shan fama ƙwarai da gaske, da shan ɗauri, na sha dūka marar iyaka, na sha hatsarin mutuwa iri iri.
Amma kafin wannan duka, za su kama ku, su tsananta muku. Za su miƙa ku ga majami'u da kurkuku, su kuma kai ku a gaban sarakuna da mahukunta saboda sunana.
Kada ka ji tsoron wuyar da za ka sha. Ga shi, Iblis yana shiri ya jefa waɗansunku a kurkuku don a gwada ku, za ku kuwa sha tsanani har kwana goma. Ka riƙi amana ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka kambin rai.