Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 5:14 - Littafi Mai Tsarki

14 Masu ba da gaskiya sai ƙaruwa suke ta yi ga Ubangiji fiye da dā, jama'a masu yawan gaske mata da maza.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Duk da haka, maza da matan da suke gaskata ga Ubangiji sai ƙaruwa suke, suka kuma ƙaru a yawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 5:14
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

suna yabon Allah, suna da farin jini a wurin dukan mutane. Kowace rana kuma Ubangiji yana ƙara masu waɗanda ake ceta.


Ba sauran cewa Bayahude ko Ba'al'umme, ko ɗa, ko bawa, ko namiji ko mace. Ai, dukkanku ɗaya kuke, na Almasihu Yesu.


har na tsananta wa masu bin wannan hanya, ina karkashe su, ina ɗaure mutane maza da mata, ina jefa su a kurkuku.


Labari ya bazu a dukan Yafa, mutane da yawa kuwa suka gaskata da Ubangiji.


Duk mutanen Lidda da na ƙasar Sarona kuwa suka gan shi, suka juyo ga Ubangiji.


Sa'an nan ne Ikkilisiyar duk ƙasar Yahudiya, da ta Galili, da ta Samariya ta sami lafiya, ta ingantu sosai, suna tafiyar da al'amuransu da tsoron Ubangiji, Ruhu Mai Tsarki na taimakonsu, har suka yawaita.


ya roƙe shi ya yi masa wasiƙu zuwa majami'un Dimashƙu, don in ya sami masu bin wannan hanya, mata ko maza, yă zo da su birnin Urushalima a ɗaure.


Amma da suka gaskata bisharar da Filibus ya yi a kan Mulkin Allah, da kuma sunan Yesu Almasihu, duka aka yi musu baftisma mata da maza.


Amma Shawulu ya yi ta yi wa Ikkilisiya ɓarna ƙwarai da gaske, yana shiga gida gida, yana jan mata da maza, yana jefa su a kurkuku.


Maganar Allah kuwa sai ƙara haɓaka take yi, yawan masu bi kuma a birnin Urushalima sai ta ƙaruwa yake yi ƙwarai da gaske, firistoci masu yawan gaske kuma suka yi na'am da bangaskiyar nan.


Amma da yawa daga cikin waɗanda suka ji wa'azin sun ba da gaskiya, har jimillarsu ta kai wajen mutum dubu biyar.


Waɗanda suka ya na'am da maganarsa kuwa aka yi musu baftisma. A ran nan kuma suka ƙaru da mutum wajen dubu uku.


“Za su ce ta wurina kaɗai Za a iya samun nasara da ƙarfi, Amma dukan waɗanda suka raina ni za su sha kunya.


A ran ɗaya ga watan bakwai, sai Ezra, firist, ya kawo Attaura a gaban taron jama'a, mata da maza, da dukan waɗanda za su ji, su fahimta.


Sa'ad da Ezra yake yin addu'a, yana hurta laifi, yana kuka, yana a durƙushe gaban Haikalin Allah, sai babban taron jama'a, mata, da maza, da yara daga Isra'ila suka taru wurinsa. Mutane suka yi kuka mai zafi.


Ya kuma rarraba wa dukan taron jama'ar Isra'ila, mata da maza, ƙosai, da nama, da zabibi, sa'an nan dukan mutane suka watse, kowa ya tafi gidansa.


Sai dukan mata da maza waɗanda suke da niyya, suka kawo kayayyakin ƙawanya, wato da 'yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri iri. Kowane mutum ya ba da sadaka ta zinariya ga Ubangiji.


domin shi mutum ne nagari cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya. Sai mutane masu yawan gaske suka ƙaru ga Ubangiji.


Ina kuma jiyayyar Almasihu da iblis? Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ