Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 4:24 - Littafi Mai Tsarki

24 Su kuwa da jin haka, sai suka ɗaga muryarsu ga Allah da nufi ɗaya, suka ce, “Ya Mamallaki, Mahaliccin sama, da ƙasa, da teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

24 Sa’ad da suka ji wannan, sai suka ɗaga muryoyinsu gaba ɗaya cikin addu’a ga Allah, suka ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kai ka halicci sama da ƙasa da kuma teku, da kome da yake cikinsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 4:24
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Gama cikin kwana shida Ubangiji ya yi sama, da duniya, da teku, da dukan abin da yake cikinsu, amma a rana ta bakwai ya huta. Soboda haka Ubangiji ya keɓe ranar Asabar, ya tsarkake ta.


“Ya Ubangiji Allah, kai ne ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka da ƙarfinka, ba abin da ya fi ƙarfinka.


Sa'an nan suka yi wannan addu'a, suka ce, “Kai kaɗai ne Ubangiji, ya Ubangiji, Kai ne ka yi samaniya da taurari da sararin sama. Kai ne ka yi ƙasa, da teku, da kowane abu da yake cikinsu, Ka ba dukansu rai, Ikokin samaniya sun rusuna suna maka sujada.


Sa'an nan ya yi addu'a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji Allah na Isra'ila, kai da kake zaune a kan gadon sarautarka, kai kaɗai ne Allah a dukan mulkokin duniya, kai ne ka yi sama da ƙasa.


Ku raira waƙa ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Gama ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannun mugaye.


Ubangiji ya ce, “Ni ne wanda yake ƙarfafa ku. Don me za ku ji tsoron mutum mai mutuwa, Wanda bai fi ciyawa tsawon rai ba?


Yanzu ya Ubangiji Allahnmu, ina roƙonka ka cece mu daga hannunsa domin dukan mulkokin duniya su sani kai kaɗai ne Allah, ya Ubangiji.”


A wajen tsakar dare Bulus da Sila suna addu'a suna waƙoƙin yabon Allah, 'yan sarka kuwa suna sauraronsu,


Da aka sau su, suka tafi wurin mutanensu, suka ba su labarin duk abin da manyan firistoci da shugabanni suka faɗa musu.


“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ