Da kuma suka daɗa yi musu kashedi, suka sake su, don sun rasa yadda za su hore su saboda jama'a, domin dukan mutane suna ɗaukaka Allah saboda abin da ya auku.
suka ce, “Yaya za mu yi da mutanen nan? Don hakika sanannen abu ne ga dukan mazauna Urushalima, cewa an yi wata tabbatacciyar mu'ujiza ta wurinsu, ba mu kuwa da halin yin mūsawa.