Da Bitrus ya ga haka, sai ya yi wa jama'a jawabi, ya ce, “Ya ku 'yan'uwa Isra'ilawa, don me kuke mamakin wannan? Don me kuma kuke ta dubanmu, sai ka ce da ikon kanmu ne, ko kuwa don ibadarmu muka sa shi tafiya?
Shi kuwa ya zura masa ido a tsorace, ya ce, “Ya Ubangiji, mene ne?” Mala'ikan kuma ya ce masa, “Addu'arka da sadakarka sun kai har a gaban Allah, abubuwan tunawa ne kuma a gare shi.