12 Da muka zo Sirakusa muka kwana uku a nan.
12 Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku.
Bayan wata uku muka tashi a cikin wani jirgin Iskandariya, wanda ya ci damuna a nan tsibirin. An kuwa yi masa alama da surar Tagwaye Maza.
Daga nan kuma muka zaga sai ga mu a Rigiyum. Da muka kwana, iska ta taso daga kudu, kashegari kuma muka kai Butiyoli.
Da muka gama tafiyarmu daga Taya, muka isa Talamayas, muka gaisa da 'yan'uwa, muka kuma kwana ɗaya a wurinsu.
Da muka shiga wani jirgi na Adaramitiya, mai shirin tashi zuwa waɗansu garuruwan da suke gaɓar Asiya, muka fara tafiya. Aristarkus kuwa, wani mutumin Tasalonika ta ƙasar Makidoniya, na tare da mu.