7 Amma shugaba Lisiyas ya zo ya ƙwace shi daga hannunmu ƙarfi da yaji,
Har ma yana nema ya tozarta Haikali, amma muka kama shi. [Niyyarmu ce mu hukunta shi bisa ga shari'armu.
ya yi umarni masu ƙararsa su zo a gabanka.] In kuwa ka tuhume shi da kanka, za ka iya tabbatarwa daga bakinsa duk ƙarar da muke tāsarwa.”
Mugaye ba su iya yin barci, sai sun aikata ɓarna. Ba su barci sai sun cuci wani.
Suna neman kashe shi ke nan, sai labari ya kai ga shugaban ƙungiyar yaƙi, wai Urushalima duk ta hargitse.
Da Bulus ya zo ga bakin matakala, sai da soja suka kinkime shi saboda haukan taron,
Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.
Sa'an nan ya kira jarumi biyu ya ce, “Ku shirya soja metan, da barade saba'in, da 'yan māsu metan, su tafi Kaisariya da ƙarfe tara na daren nan.”