Ayyukan Manzanni 24:24 - Littafi Mai Tsarki24 Bayan 'yan kwanaki Filikus ya zo tare da matarsa, Durusila, wata Bayahudiya. Sai ya aika a zo da Bulus, ya kuwa saurare shi a kan maganar gaskatawa da Almasihu Yesu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202024 Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
da yake mun sani mutum ba ya samun kuɓuta ga Allah ta wurin bin Shari'a, sai dai ta wurin gaskatawa ga Yesu Almasihu kaɗai, mu ma mun gaskata da Almasihu Yesu, domin mu sami kuɓuta ga Allah ta wurin bangaskiya ga Almasihu, ba ta wurin bin Shari'a ba, don ba ɗan adam ɗin da zai sami kuɓuta ga Allah ta hanyar bin Shari'a.