Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 24:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Saboda haka, a kullum nake himma in kasance da lamiri marar abin zargi a wurin Allah da wurin mutane.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 24:16
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Bulus ya zuba wa majalisar ido ya ce, “Ya ku 'yan'uwa, bautar Allah nake yi da lamiri mai kyau har ya zuwa yau.”


Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.


Ba ruwanmu da ɓoye-ɓoye na munafunci, ko makirci, ko yi wa Maganar Allah algus, amma ta wurin bayyana gaskiya a fili, sai kowane mutum ya shaidi gaskiyarmu a lamirinsa a gaban Allah.


sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.


Ayyukansu sun nuna, cewa abin da Shari'a ta umarta a rubuce yake a cikin zukatansu, lamirinsu kuwa yana shaidawa, tunaninsu kuwa yana zarginsu, ko kuma yana kāre su.


Fariyarmu ke nan, lamirinmu yana ba da shaida, cewa mun yi zaman tsarki a duniya da zuciya ɗaya, tsakani da Allah, tun ba ma a gare ku ba, ba bisa ga wayo irin na ɗan adam ba, sai dai bisa ga alherin Allah.


Baftisma kuwa, wadda ita ce kwatancin wannan, ta cece ku a yanzu, ba ta fitar da dauɗa daga jiki ba, sai dai ta wurin roƙon Allah da lamiri mai kyau, ta wurin tashin Yesu Almasihu daga matattu,


Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.


Ban sani ina da wani laifi ba, amma ba don wannan na kuɓuta ba, ai, Ubangiji shi ne mai gwada ni.


Ku kuma kasance da lamiri mai kyau, don in an zage ku, waɗanda suka kushe kyakkyawan halinku na bin Almasihu su kunyata.


Ai, abin karɓa ne, in saboda mutum yana sane da nufin Allah, ya jure wa wuyar da yake sha, ba da alhakinsa ba.


Ku yi mana addu'a, gama mun tabbata muna da lamiri mai kyau, muna kuwa so mu tafiyar da al'amuranmu da halin kirki ne.


balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.


Ina gode wa Allah, wanda nake bauta wa da lamiri mai tsabta, kamar yadda kakannina suka yi, duk sa'ad da nake tunawa da kai a cikin addu'ata ba fāsawa.


Ku shaidu ne, haka kuma Allah, game da irin halin da muka nuna muku, ku masu ba da gaskiya, wato halin tsarki da na adalci da na rashin aibu.


Lalle ne su riƙi asirin bangaskiya da lamiri mai tsabta.


kana riƙe da bangaskiya da lamiri mai kyau. Gama waɗansu mutane, saboda ƙin kasa kunne ga lamirinsu, suka lalatar da bangaskiyarsu.


Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida,


Kada ku zama abin tuntuɓe ga Yahudawa ko al'ummai ko ikkilisiyar Allah,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ