Da ya zo, Yahudawan da suka zo daga Urushalima suka kewaye shi a tsaitsaye, suna ta kawo ƙararraki masu yawa masu tsanani a game da shi, waɗanda ma suka kasa tabbatarwa.
A sa'ad da ya isa Ƙofar Biliyaminu, shugaban matsara, Irija ɗan Shelemiya, ɗan Hananiya, ya kama annabi Irmiya ya ce, “Kai kana gudu zuwa wurin Kaldiyawa ne.”