Aka faɗa wa Dawuda cewa, “Ahitofel yana cikin 'yan maƙarƙashiya tare da Absalom.” Sai Dawuda ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubangiji, ina roƙonka, ka wofintar da shawarar Ahitofel.”
Lokacin da Absalom yake miƙa hadaya, sai ya aika zuwa Gilo a kira masa Ahitofel Bagilone mai ba Dawuda shawara. Maƙarƙashiyar kuwa ta yi ƙarfi. Mutane masu haɗa kai da Absalom suka riƙa ƙaruwa kullum.