Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 22:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Da jarumin ɗin ya ji haka, sai ya je ya shaida wa shugaban, ya ce, “Me kake shirin yi ne? Mutumin nan fa Barome ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 22:26
5 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bayan haka mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, suna kuma gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji cewa shi Barome ne.


Saboda haka, waɗanda suke shirin tuhumarsa, suka rabu da shi nan da nan. Shi ma shugaban da ya fahimci Bulus Barome ne, sai ya tsorata, ga shi kuwa, ya ɗaure shi.


Sai ƙungiyar soja da shugabansu, da dogaran nan na Yahudawa suka kama Yesu, suka ɗaure shi,


Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da 'yancin Roma bulala, ba ko bin ba'asi?”


Sai shugaban ya zo ya ce wa Bulus, “Faɗa mini gaskiya, kai kuwa Barome ne?” Sai ya ce, “I”.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ