Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayyukan Manzanni 22:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Bayan sun ɗaɗɗaure shi da tsirkiya, Bulus ya ce wa jarumin ɗin da yake tsaye kusa, “Ashe, ya halatta a gare ka ka yi wa mutumin da yake da 'yancin Roma bulala, ba ko bin ba'asi?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayyukan Manzanni 22:25
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma Bulus ya ce musu, “Ai, a fili suka daddoke mu, ba ko bin ba'asi, mu ma da muke Romawa bisa ga 'yangaranci, suka jefa mu a kurkuku, yanzu kuma sā fitar da mu a ɓoye? Sai dai su zo da kansu su fito da mu.”


Ni kuwa na amsa musu na ce, ba al'adar Romawa ba ce a yi wa wani hukunci, don faranta wa wani rai, ba tare da masu ƙarar, da wanda aka kai ƙara, sun kwanta a gaban shari'a ba, ya kuma sami damar kawo hanzarinsa game da ƙarar da aka tāsar.


Amma jarumin da ya so ya ceci Bulus, ya hana i da nufinsu, ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci,


Bulus kuwa ya kira wani jarumi ya ce, “Ka kai saurayin nan wurin shugaba, yana da wata magana da zai faɗa masa.”


Kashegari ga mu a Sidon. Yuliyas kuwa ya yi wa Bulus alheri, ya ba shi izini ya je ya gano abokansa, su yi masa taimako.


Da aka shirya mu tashin jirgin ruwa zuwa ƙasar Italiya, sai suka danƙa Bulus da waɗansu 'yan sarƙa a hannun wani jarumi, mai suna Yuliyas, na ƙungiyar Augustas.


An yi wani mutum a Kaisariya, mai suna Karniliyas, wani jarumi ne na ƙungiyar soja da ake kira Ƙungiyar Italiya.


Sa'ad da jarumin da waɗanda suke tare da shi suna tsaron Yesu suka ga rawar ƙasa da kuma abin da ya auku, sai duk tsoro ya kama su, suka ce, “Hakika wannan Ɗan Allah ne!”


Sai jarumin, ya ce, “Ya Ubangiji, ban isa har ka zo gidana ba, amma sai ka yi magana kawai, yarona kuwa zai warke.


Ku yi hankali da mutane, don za su kai ku gaban majalisa, su kuma yi muku bulala a majami'arsu.


Da jarumin ɗin ya ji haka, sai ya je ya shaida wa shugaban, ya ce, “Me kake shirin yi ne? Mutumin nan fa Barome ne.”


Bayan haka mutumin nan, Yahudawa sun kama shi, suna kuma gab da kashe shi, sai na yi farat na je da soja na ƙwato shi, saboda na ji cewa shi Barome ne.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ