duk da haka dai hankalina bai kwanta ba, domin ban tarar da ɗan'uwana Titus a can ba, saboda haka, sai na yi bankwana da su, na zarce na tafi Makidoniya.
To, lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansu, ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka kuwa ba ni kaɗai nake ba, domin Uba na tare da ni.
Sai ya tashi, ya taho wurin ubansa. Amma tun yana daga nesa, sai ubansa ya hango shi, tausayi ya kama shi, ya yiwo gudu, ya rungume shi, ya yi ta sumbatarsa.