Sai manzanni da dattawan Ikkilisiya, tare da dukan 'yan Ikkilisiya, suka ga ya kyautu su zaɓi waɗansu daga cikinsu, su aike su Antakiya tare da Bulus da Barnaba. Sai suka aiki Yahuza, wanda ake kira Barsaba, da kuma Sila, shugabanni ne cikin 'yan'uwa,
Sai duk taron mutane suka yi tsit, suka saurari Barnaba da Bulus, sa'ad da suke ba da labarin mu'ujizai da abubuwan al'ajabi, da Allah ya yi ga al'ummai ta wurinsu.
An kuwa sha gaya musu labarinka, cewa kai ne kake koya wa dukan Yahudawan da suke cikin al'ummai su yar da Shari'ar Musa. Wai kuma kana ce musu kada su yi wa 'ya'yansu kaciya, ko kuwa su bi al'adu.