Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu.
Da wani saurayi a zaune a kan taga, mai suna Aftikos, sai barci ya ci ƙarfinsa sa'ad da Bulus yake ta tsawaita jawabi, da barci mai nauyi ya kwashe shi, sai ya faɗo daga can hawa na uku, aka ɗauke shi matacce.